30 Satumba 2026 - 21:16
Source: ABNA24
Gaza: Shahadar Falasɗinawa 5 Da Jikkatar 15 A Harin Isra’ila Kan Wata Motar Fararen Hula

Sojojin gwamnatin Sahayoniya da tsakar ranar yau Laraba tare da kai hari kan wata mota ta fararen hula a birnin Gaza, sun aikata wani sabon laifin ta’addanci kan fararen hular Falasɗinawa wanda sakamakonsa Falasɗinawa biyar sun yi shahada da jikkatar 15.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ƙungiyar "Hilal Ahmar ta Falasɗinu" a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa ƙungiyoyin likitanci na wannan ƙungiyar sun kai gawar shahidai biyar zuwa Asibitin Al-Shifa a birnin Gaza da wadanda suka samu raunuka 15 zuwa Asibitin Al-Quds. Wannan lamari ya faru ne bayan harin sama na gwamnatin Sahayoniya kan wata mota a yankin majalisar ministocin a unguwar Tal al-Hawa a kudu maso yammacin birnin Gaza.

Majiyoyin Falasɗinawa sun tabbatar da cewa wani jirgin yaƙi na gwamnatin Sahayoniya ya kai hari kan wata mota ta fararen hula a lokacin da take tafiya kusa da majalisar ministocin Falasɗinu da yammacin yau.

Sojojin gwamnatin Sahayoniya a kwana ta 356 a jere suna keta yarjejeniyoyin dakatar da wuta da kwanciyar hankali a Zirin Gaza waɗanda aka sanya hannu a ranar 10 ga Oktoba 2025 tare da shiga tsakanin Larabawa da Amurka a Sharm el-Sheikh na Masar.

Waɗannan hare-hare suna ci gaba ne a lokacin da yarjejeniya da fahimtar da aka yi kwanan nan a watan Yuli 2026 masu alaƙa da aiwatar da mataki na biyu na dakatar da bue wuta ke ci gaba.

Jiya Talata ma Falasɗinawa takwas sun yi shahada kuma gommai sun ji rauni. Waɗannan asarar rayuka sun faru ne a karo na 18 na keta dakatar da bude wuta gwamnatin Sahayoniya waɗanda suka haɗa da harbi daga motocin sulke da tankuna, hare-haren sama da tayar da bama-bamai da lalata gidaje da wuraren fararen hula.

Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta bayyana cewa cikin sa'o'i 24 da suka gabata an kai gawar shahidai 9 da wadanda suka jikkata 31 zuwa asibitocin Zirin Gaza.

Wannan ma'aikatar a cikin rahotonta na ƙididdiga na yau da kullum ta bayyana cewa ƙididdigar yau da kullum ta haɗa da sabbin shahidai takwas da wata mata shahida da tai shahada sakamakon tsananin raunin da ta samu. Adadin waɗanda suka ji rauni ma ya kai 31.

Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta yi nuni da cewa jimillar shahidai tun lokacin dakatar da bude wuta a ranar 11 ga Oktoba 2025 sun kai shahidai 1,431 da raunuka 5,026. Bugu da ƙari, an fitar da gawar shahidai 834 daga ƙarƙashin buraguzan gine-gine.

Wannan ma'aikatar ta yi nuni da cewa jimillar ƙididdiga tun farkon mamayewar gwamnatin Sahayoniya kan Zirin Gaza a ranar 7 ga Oktoba 2023, sun kai shahidai 74,032 da jikkatar 175,142.

…………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha